Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro kan samun masaniya dangane da hanyoyin tarjamar kur’ani mai tsarki a kasar Pakistan wanda zai samu halartar masana da malamai da suke gudanar da ayyuka a fagage da daman a kur’ani mai tsarki a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo IIU, cewa za a gudanar da wani zaman taro kan samun masaniya dangane da hanyoyin tarjamar kur’ani mai tsarki a kasar Pakistan wanda zai samu halartar masana da malamai da suke gudanar da ayyuka a fagage da daman a kur’ani mai tsarki a kasar ta Pakistan da take bayar da gagagrumar gudunmawa ta wannan bangare.
A wani labarin kuma wani daya daga cikin mutanen kasarFaransa da suka karbi addinin Musulunci ya halarci taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Tehran tare da halartar cibiyoyin Musulunci daga kasashen musulmi da na larabawa da ma wasu kasashen nahiyar Asia.
Daga cikin manyan jami’an jamhuriyar muslunci ta ta halarci wurin taron baje kolin kur’ani ta yi kira da a fadada fikirar nan ta fadakar al’ummar musulmi zuwa fadakar yan adamataka tsakanin mutane domin kuwa kur’ani mai tsarki ya zo ne domin shiryar da dukkanin mutane baki daya saboda haka duk wata rahma da take tatatre da alk’r'ani tana shafar mutane ne da suke rauwa a doron kasa kamar dai yadda hakan yake a cikin littafin mai tsarki.
1076015