Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sdarwa na yanar gizo, cewa ana samun karuwar masallatai a birnin Dubai babbar cibiyar kasuwanci ta kasar hadaddiyar daular larabawa a cikin shekaru hudu da suka gabata kamar dai yadda ma’aikatar klula da harkokin addini reshenta a birnin ta bayyana cewa adadin ya karu da kashi 36 cikin dari na addadin masattan da ke birnin na Dubai.
A can kasar faransa kuwa majalisar mabiya addinin muslunci a kasar za ta shigar da kara kan mutanen da suek nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai da suke zaune a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen nahiyar turai da suka fi yawan musulmi, ta yadda adadinsu ya zama su ne na biyu ta fuskacin yawa a kasar bayan mabiya addinin kiristanci, amma kuma duk da haka har yanzu gwamnatin kasar ba ta amince da addinin musulunci a hkumance ba amatsayin daya daga cikin addinain kasar, duk kuwea da cewa ta amince da addinin yahudanci.
Shigar da kara kan mutanen da suke nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai, yin hakan zai zama tamkar wani hannunka mai sanda ga sauran masu irin wannan akida.
1079521