IQNA

Taron Girmama Wadanda Suka Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Mai Tsarki A Algeria

22:43 - August 16, 2012
Lambar Labari: 2394561
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron girmama wadanda suka gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Algeria tare da halartar shugaban kasar a babban masallacin Algiers wanda taron ya samu halartar malaman addini da kuma wakilan cibiyoyi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Algeris, cewa an gudanar da taron girmama wadanda suka gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Algeria tare da halartar shugaban kasar a babban masallacin Algiers wanda taron ya samu halartar malaman addini da kuma wakilan cibiyoyi na addini na kasar.
A cikin wannan makon an gudanar da wani zaman taro a birnin Istanbul na kasar Turkiya musamman domin yin bayani kan matsayin Sayyida Fatima Zahra da kuma falalolinta gami da kyawawan halayenta da darussan da rayuwarta ke koyar da dan adam musamman ma mata.
Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa a Amurka wadda mabiya addinin muslunci da suke zaune a kasar za su gudanar a babban ginin cibiyar muslunci da ke birnin Washington fadar mulkin kasar ta Amurka, wadda akasarin mazauna cikinta mabiya addinin kirista ne.
adadin masallatai ya karu da kashi 74 cikin dari a kasar Amurka kamar dai yadda wani rahoto ya nuna wanda kungiyar jama’at Iman ta watsa a yau da ke cewa wannan adadi ya karu ne a cikin shekaru goma da suka gabata har zuwa karshen shekara ta dubu da sha daya. 1079364

captcha