Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa sarkin Saudiyya ya gabatar da wata shawara a gaban taron da ya kira na gaggawa a birnin Makka mai alfarma domin tattauna batun Syria da kuma raba wasu daga cikin batutuwa kamar palastinu da kuma halin da musulmin kasar Myanmar suke ciki duk da cewa wannan ba ita ce manufar taron ba.
An gudanar da wani zaman taro a birnin Pretown na kasar saliyo da nufin tunawa da marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran tare da yin gwagwarmaya da makiya muslunci da all’ummar musulmi, kama daga sarki Shah har zuwa babban shaidan da kuma haramtacciyar kasar yahudawa.
Bangare guda kuma ana shirin gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan irin gudunmawar da marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda ya bayar wajen ci gaban al’ummar musulmi da kuma fadakarta a wannan karni da muke cikinsa.
A yayin wannan taro za a gabatar da jawabai wanda malamai da kuma masana gami da malaman jami’oi da maruta za su gabatar, inda za a yi bayani kan matsayinsa na ilimi da kuma irin gwagwarmayar da ya yi da manyan kasashen duniya ‘yan mulkin mallaka, wadanda suke danne sauran al’ummomin duniya tare da dora manufofin siyasarsu kan duniya bisa zalunci.
1079234