IQNA

Kisan Da Aka Yi Kan Musulmin Myanmar Za A Tattauna Shi A majalisar Dinkin Duniya

17:39 - August 17, 2012
Lambar Labari: 2394987
Bangaren kasa da kasa, kisan da aka yi musulmin kasar Myanmar zai zama cikin muhimman abubuwan da za a tattauna su a gaban taron bababn zauren majalisar diniin duniya kamar dai yadda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar a taron da ta gudanar da siyasa a birnin Makka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nouvelobs, cewa kisan da aka yi musulmin kasar Myanmar zai zama cikin muhimman abubuwan da za a tattauna su a gaban taron bababn zauren majalisar diniin duniya kamar dai yadda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar a taron da ta gudanar da siyasa a birnin Makka a cikin wannan makobayan da kasashen yammacin turai suka bukaci mahukuntan Saudiyya da su kira zaman taron.
Kwamitin kula da ayyuka na hadin gwiwa tsakanin kasashen msuulmi masu gudanar d ayyuka da suka shafi dukkanin bangarori ya gudanar da zamansa a birnin Astaneh na kasar Qazagystan tare da halartar wakilai daga kasashe mambobi a cikinsa.
An bude wani ofishin kula da harkokin addini na kasar Kyrgystan a kasar Kuwait da nufin kara bunkasa harkokin addini da kuma kyakyawar alaka tsakanin kasashen ta fuskkar bunksa harkokin addini da ilim ga mi da al’adu a tsakaninsu kasantuwarsu mambobi a cikin kungiyar kasashen musulmi.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba.
1080680















captcha