Bangaren kasa da kasa, dubban mutane ne suke ci gaba da gudanar da jerin gwanon ranar Qods a birnin Karbala mai alfarma akaar Iraki domin raya wannan rana mai matukar muhimmanci ga dukaknin musulmi inda ake tunawa da wannan wuri mai albarka da yahudawan sahyuniya suke mamaye da shi tare da zimmar kwato shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a Iraki, cewa a yau dubban mutane ne suke ci gaba da gudanar da jerin gwanon ranar Qods a birnin Karbala mai alfarma akaar Iraki domin raya wannan rana mai matukar muhimmanci ga dukaknin musulmi inda ake tunawa da wannan wuri mai albarka da yahudawan sahyuniya suke mamaye da shi tare da zimmar kwato shi a lokuta masu zuwa da yardar Allah madaukakin sarki.
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta shiga cikin jerin kasashen da suka haramta kayyakin haramtacciyar kasar Isra’ila kamar yadda wasu kasashe suka dauki irin wannan matakin tun da jimawa domin nuna rashin amincewarsu da zaluncin da take yi kan al’ummar palastinu marassa kariya kamar dai yadda yhaudawan sahyuniya suka shahara da hakan.
An shirya kara da za agabatar a gaban shari’a kan wasu yahudawan sahyuniya masu wulakanta kur’ani mai tsarki a cikin yankunan palastinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye domin tabbatar musu da cewa musulmi ba za su amince da abin da uke yi ba na keta alfarma kur’ani da sauran ababe masu alfarma a cikin addinin muslunci. 1080385