IQNA

Gwamnatin Kasar Jamus Ta Taya Musulmin Kasar Murnar Salla

23:05 - August 18, 2012
Lambar Labari: 2395903
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Jamus ta taya mabiya addinin muslunci murnar zagayowar lokutan da suke gudanar da tarukan idin karamar salla kamar dai yadda suka sabayi karshen kowane wata na ramadan mai alfarma.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo, cewa gwamnatin kasar Jamus ta taya mabiya addinin muslunci murnar zagayowar lokutan da suke gudanar da tarukan idin karamar salla kamar dai yadda suka sabayi karshen kowane wata na ramadan mai alfarma daidai da sauran musulmi na duniya.
Kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta yi suka dangane da ziyarar da wasu daga cikin fitatun maamai suka kai a birnin Qods tare da hadin baki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman ma babban malamin kasar Masar Ali Juma’a wanda kuma shi ne ake yin koyi da shi a matsayin malamin addini.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti.
1080766
captcha