Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iba, cewa al’ummar musulmi sun gudanar da sallar idi na karamar salla awannan shekara a tsakanin hubbarori biyu masu albarka da suke garin Karbala mai alfarma wanda hakan ya zama daya daga cikin muhimman lamurra da sallar ta bana ta kebanta da su a wannan shekara kamar dai yadda rahotan ya tababtar.
A bangare guda kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa; batun Qudus yana daga cikin muhimman al'amuran da suka shafi dukkanin al'ummar musulmin duniya. A jawabin da ya gudanar a yayin ganawarsa da daruruwan tsoffin fursunonin yaki na kasar Iran a jiya laraba; Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewa; halartar zanga zangar ranar Qudus ta duniya cikin hamasa lamari ne da zai zame babban martani kuma kalubale ga makiya addinin Musulunci da al'ummar Palasdinu.
Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kuma bayyana cewar mamaye Palasdinu tare da tsugunar da yahudawan sahayoniyya a cikinsa shi ne tushen bullar sharri da matsaloli a yankin gabas ta tsakiya. Jagoran ya kara da cewar ba don makircin da aka kulla na samar da haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin gabas ta tsakiya ba, da duk ba a kai ga fuskantar matsalolin yake- yake, sabani tsakanin kasashe da tsoma bakin 'yan mulkin mallaka masu girman kai a yankin ba.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin na Musuluncin ya jaddada cewa; Yahudawan sahayoniyya da masu goya musu baya suna iyaka kokarinsu na ganin sun mantar da al'umma batun Palasdinu, don haka wajibi ne a kan al'ummar musulmin duniya su mike tsaye domin fuskantar wannan makirci da yaudara.
1082222