IQNA

Mutane Sun Gudanar Da Wani Samfuri Na Kotun Hukunta Sarkin Bahrain

22:12 - August 21, 2012
Lambar Labari: 2396722
Bangaren kasa da kasa, dubban mutabne za su yi wani gangami inda aka kafa wata kotu ta jeka na yi ka domin hukunta sarkin kasar Bahrain dangane da kisan gillar da yake kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana a kasar tun tsawon shekara guda da rabi da suka gabata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na cikin gida, cewa dubban mutabne za su yi wani gangami inda aka kafa wata kotu ta jeka na yi ka domin hukunta sarkin kasar Bahrain dangane da kisan gillar da yake kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana a kasar tun tsawon shekara guda da rabi da suka gabata kuma za a yi hu8kuncin ne a gaban ofishin jakadancin kasar da ke birnin Tehran.
Bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman ahkkokinsu da aka haramta musu.
Bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta kwana da sanin cewa, duk abin da ya samu malamin to zai kare a kanta ne.
Al’ummar Bahrain dai kamar sauran al’ummomin larabawa suna neman hakkokinsu ne da aka haramta musu ta hanyar lumana, amma mahukuntan kasar tare da na kasar Saudiyya da kuma taimakon Amurka da Birtaniya, suna ci gaba da murkushe masu zanga-zangar.
1082286


















captcha