IQNA

Ci Gaban Da Iran Ta Samu Domin Samar da Hanyar Tabbatar Da Adalci Ne

22:08 - August 21, 2012
Lambar Labari: 2396733
Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran ya bayyana cewa ci gaban da Iran take samu a halin yanzu share hanya ne na tabbatar adalci a bayan kasa ba na bayar da tsoro ba ne ko firgita wasu ko kuma mamaye yankunan wasu al’ummomi saboda haka sauran al’ummomi su kwantar da hankalinsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa Mahmud Ahmadinejad shugaban kasar Iran ya bayyana cewa ci gaban da Iran take samu a halin yanzu share hanya ne na tabbatar adalci a bayan kasa ba na bayar da tsoro ba ne ko firgita wasu ko kuma mamaye yankunan wasu al’ummomi saboda haka sauran al’ummomi su kwantar da hankalinsu kuma su mayar da komai ga ubangiji.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramtawa kiristocin kasar Masar shiga zuwa ziyara abirnin Qods mai alfarma saboda canjin siyasar da aka samu a kasar Masar a cikin wannan lokaci bayan hambarar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar wanda ya ke dasawa da yahudawa da Amurka gami da gwamnatin wahabiyawan saudiyya.
Wani labarin kuma daga Masar ya yi nuni da cewa, karon farko za a fitar da jaridar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa wadda kuma za ta fara fito nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran jam’iyyar Gadir ta kasar Masar kumababban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar masar Muhammad Duraini shi ne ya bijiro da batun bude wannan jaridar, kuma zai bayar da gagarumar gudunmawarsa domin ci gabanta.
1082621





















captcha