IQNA

Masana A Tunisia Sun Yi Gargadi Dangane Yaduwar Akidar Wahabiyanci A kasar

22:49 - August 22, 2012
Lambar Labari: 2397242
Bangaren kasa da kasa, masana a kasar Tunisia sun yi gargadi dangane da yaduwar akidar wahabiyanci wadda ta ginu a kan kafirta sauran musulmi tare da ware makudan kudade da kasashen Saudiyya da da Qatar suke yi wajen yada wannan mummunar akida da ta ginu a kan bata da nisa da addiin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa masana a kasar Tunisia sun yi gargadi dangane da yaduwar akidar wahabiyanci wadda ta ginu a kan kafirta sauran musulmi tare da ware makudan kudade da kasashen Saudiyya da da Qatar suke yi wajen yada wannan mummunar akida da ta ginu a kan bata da nisa da addiin muslunci na hakika.
Da dama daga cikin malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma an ya nakalto daga shafin sadrawa an yanar gizo na Nun cewa, Fathi shazili tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa.
Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu, sakamakon danne su da wahabiyan kasar.
1082979



















captcha