Bangaren kasa da kasa, abin da Allah ya bukata daga dukkanin mutane shi ne bin sahihin tafarki na addininsa da ya aiko manzonsa tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da shi amma rashin bin wannan sahihin tafarki ne ya kai ga samun wasu jama’a da ba su kaan tafarkin addini suna magana da yawunsa kuma suna batar da mutane.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin makaranta kur’ani ya sheda cewa abin da Allah ya bukata daga dukkanin mutane shi ne bin sahihin tafarki na addininsa da ya aiko manzonsa tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da shi amma rashin bin wannan sahihin tafarki ne ya kai ga samun wasu jama’a da ba su kaan tafarkin addini suna magana da yawunsa kuma suna batar da mutane da sunan addini, wato akidar nan ta wahabiyanci da ke kafirta sauran musulmi.
Malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar.
Kuma an ya nakalto daga shafin sadrawa an yanar gizo na Nun cewa, Fathi shazili tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa.
1082134