Bangaren kasa da kasa, kungiyar palastinawa ta Hamas ta wata barazana da ke cewa ba za ta taba daina kalubalantar yahudawan sahyuniya kan batun masallacin Qods mai alfarma ba kuma ba za ta taba barin yahudawan su ci gaba da keta alfarmar wannan wuri mai tsarki ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine Info, cewa kungiyar palastinawa ta Hamas ta wata barazana da ke cewa ba za ta taba daina kalubalantar yahudawan sahyuniya kan batun masallacin Qods mai alfarma ba kuma ba za ta taba barin yahudawan su ci gaba da keta alfarmar wannan wuri mai tsarki ba kamar yadda ba ta yi hakan a baya ba.
daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su ba tare da laifin tsaye ko na zaune ba.
Matasan sun taru ne a wani babban dandali da ke tsakiyar birnin Moscow na kasar Rasha inda suka daga tutoci na kasashen Rasha da kuma palastinedomin nuna cikakken goyon bayansu ga wannan al’umma da take fuskantar zalunci daga yahudawan sahyuniya, tare da amincewa manyan kasashe na duniya kama su Amurka da Birtaniya gami da Faransa da sauransu.
Wadannan daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su da yin kisan gilla a kansu.
1083117