Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa an fuskanci babar matsala dangane da ficewar dubban masu ziyara a kasar Iraki da suke cikin kasar a lokacin da aka fara hutun kwanaki goma akasar wanda hakan ya santya wasu ba za su iya samun damar fita ba domin kuwa da tikitin jigi ko kuma babu wurare a cikin jirage.
Limamin juma'a a nan birnin Tehran, ya ce kisan da makiya ke yi wa malaman kimiya na kasar, ba abin da zai cusa wa al'ummar kasar face farkawa da kuma kare martabobin kasar a kowadanne fagage na rayuwa, musamman wannan bangare na ilimimin nukiliya da Iran take ggudanar da ayyukanta a cikin na zaman lafiya domin amfanin fararen hula.
A lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a masallacin jami'ar Tehran a yau, Ayatullahi Mohammad Emami-Kashani, ya ce kisan na baya-bayan nan da makiya suka yi wa malamin kimiyyar nukiliya na kasar mai suna Mustafa Ahmadi Roshan, wata alama ce da ke kara nuna wa duniya irin damuwar da kasashe da ke hamayya da Iran din ke da ita dangane da irin ci gaba da kuma 'yancin da kasar take da shi na dogoro da kai a fannoni na bincike da kuma kimiya.
Har ila yau limamin ya ce wasu daga cikin dalilan matsa kaimi da kasashen yamma musamman ma Amurka ke yi a kan Iran, sun hada da yadda al'ummomin kasashen wannan yanki suka juya mata baya, saboda haka suke zargin Iran da hannu a shirya irin wannan bore da ke gudana.
1083197