IQNA

Muhammads Shahabi ya halarci Wani Samfurin Kotun Hukunta Sarki Bahrain

22:50 - August 22, 2012
Lambar Labari: 2397248
Bangaren kasa da kasa, gamayyar kungiyoyi na hadin gwiwar musulmi sun gudanar da wani zaman misilta kotu a birnin Tehran domin hukunta sarkin Bahrain kan kisan gillar da yake wa fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana akasar tun tsawon shekara guda da rabi ba tare da kasashen duniya sun ce uffan kan hakan ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa gamayyar kungiyoyi na hadin gwiwar musulmi sun gudanar da wani zaman misilta kotu a birnin Tehran domin hukunta sarkin Bahrain kan kisan gillar da yake wa fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana akasar tun tsawon shekara guda da rabi ba tare da kasashen duniya sun ce uffan kan hakan ba saboda abin da ake kira munafuncin siyasa.
Kungiyar gwagwarmayar kasar Lebanon ta hzib ullah ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da kai harin da jami’an tsaro gami da ‘yan bangar masarautar Baharain suka yi kan gidan sakataren jamiyar wifaq ta kasar Bahrain, a yankurin mahukuntar tare da taimakon AMURKA DA Saudiyya suke yi na ganin sun murkushe masu neman sauyi.
B bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman ahkkokinsu da aka haramta musu.
Bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta kwana da sanin cewa, duk abin da ya samu malamin to zai kare a kanta ne.
Al’ummar Bahrain dai kamar sauran al’ummomin larabawa suna neman hakkokinsu ne da aka haramta musu ta hanyar lumana, amma mahukuntan kasar tare da na kasar Saudiyya da kuma taimakon Amurka da Birtaniya, suna ci gaba da murkushe masu zanga-zangar lumana.
1083237












captcha