Bangaren kas ada kasa, sabon bugu na mujallar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a karo na ashiri a kasar Mali wadda ke dauke da bayanai da suke yin hannuka mai sanda ga musulmi kan harkokinsu na rayuwa da kuma yadda ya kamata akiyaye kaidoji da dokokin addinin muslunci a cikin dukaknin lamurran rayuwa.
Kamfanin dlalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nasakineh Ashura, cewa sabon bugu na mujallar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a karo na ashiri a kasar Mali wadda ke dauke da bayanai da suke yin hannuka mai sanda ga musulmi kan harkokinsu na rayuwa da kuma yadda ya kamata akiyaye kaidoji da dokokin addinin muslunci a cikin dukaknin lamurran rayuwa musamman a kasashen yammacin nahiyar Afirka.
A bangare guda kuma a ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
A kwanakin baya ne Yusuf Kardawi da ake kallonsa amtsayin daya daga cikin mamalan duniyar sunna, kuma daya daga cikin malaman da suka taka rawa a baya domin ganin sun wayar da kan muslulmi kan babbar barazanar da ke tattare da kulla alaka da musulmi suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a halin yanzu ya zama malamin fadar sarkin Qatar, inda yake bayar da fatawowyi da suka yi daidai da abin da sarkin kasar ke bukatar ji.
1083693