Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani na girmama wadanda suka shiga gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarkia yankin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya musamman wadanda suka nuna kwazo daga cikinsu alokacin gudanar da wannan gasa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shfin sadarwa na yanar gizo na rasid, cewa an gudanar da wani na girmama wadanda suka shiga gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarkia yankin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya musamman wadanda suka nuna kwazo daga cikinsu alokacin gudanar da wannan gasa da aka yi a yankin.
Wannan zaman taro dai babbar cibiyar kula da harkokin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ta kasr ce ta dauki nauyin shirya wannan taro, inda wasu daga cikin jami’an diplomasiiya suka samun halarta, daga ciki kuwa har jami’an ofishin jakdancin jamhuriyar musulunci ta Iran da ke kasar wadanda suka samu halarta, tare da mika godiya ga dukkanin mahalrta.
Gudanar da taron tunawa da marigayi Imam wanda ya assa jamhuriyar muslunci ta Iran wanda a ka gudanar a babban masallacin Zahra da ke garin Majonka a kasar Madagascar tare da halartar malaman addini da kuma masana na kasar, hakan na nuna irin gagarumin ci gaban da ake samu na fadaka da gane matsyin marigayi Imam da kuma irin sakon da yake dauke da shi ga al’ummar musulmi ta duniya baki daya.
1083690