IQNA

Ana Yada Kiyaya Da Musulmi A Birnin New York Na Kasar Amurka

18:01 - August 26, 2012
Lambar Labari: 2399350
Bangaren kasa da kasa, kiyayya da musulmi na ta karuwa tsakanin Amurkawa musamman a birnin New York fadar mulkin kasar sakamakon siyasar da kasar take bi ta kin musulmi da kuma takura musu saboda biyama yahudawan sahyuniya bukatrsu ta wannan hanaya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo moosly, cewa kiyayya da musulmi na ta karuwa tsakanin Amurkawa musamman a birnin New York fadar mulkin kasar sakamakon siyasar da kasar take bi ta kin musulmi da kuma takura musu saboda biyama yahudawan sahyuniya bukatrsu ta wannan hanaya kamar dai yadda hakan ya bayyana a fili.
Sabon Manzon da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Kasashen Larabawa ke shirin turawa zuwa kasar Siriya Lakhdar Brahimi, ya ce ya yi murna da karamcin da aka yi masa ta hanyar nada shi a kan wannan matsayi, to amma kuma yana cikin damuwa da kuma shakku dangane da irin kuncin da ke tattare da aiki da ke gabansa. Brahimi ya bayyana hakan ne a yammacin jiya lokacin da yake ganawa da Babban Magakatarda na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a birnin New York kafin ya gana da sauran jakadojin kasashen duniya da ke Majalisar ta Dinkin Duniya. To sai dai ya ce abu mafi muhimmaci a gare shi shi ne al'ummar kasar Siriya amma ba nuna bangaranci ko kuma son-kai a cikin aikinsa ba.
Ita dai gwamnatin kasar Siriya ta bakin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Faysal Meqdad, ta ce tuni ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya a rubuce cewa, za ta bayar da cikakken hadin-kai ga sabon Manzon nata Lakhdar Brahimi kamar dai yadda ta bai wa wadanda suka gabace shi hadin-kai.
1084249







captcha