Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, nan ba da jimawa ba za a gudanar da wani zaman taro mai taken jiran bayyana hujja a birnin London an kasar Birtaniya wanda zai samu halartar malamai da kuma masana da su gabatar da jawabai kan matsayin jiran bayyana hujjar Allah a bayan kasa da kuma matsayin wannan jira awajen Allah madaukakin sarki, wanda hakan ibada ce.
Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee, ya jaddada muhimmancin ranar Qudus ta duniya ga mutanen kasar Iran da kuma sauran al-ummar musulmin duniya. Jagoran ya bayyana haka ne a jiya lahadi a cikin khudubobinsa na sallar idi wacce a aka gudanar a masallacin jumma’a ta Jami’ar Tehran a nan birnin Tehran. Jagoran ya yaba da yadda aka gudanar da zanga zangar ranar ta Qudus a nan kasar Iran da kuma wasu kasashen duniya a ranar jumma’a da ta gabata, jumma’a ta karshe na watan Ramadan.
Fiye da shekaru 30 da suka gabata ne Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ayyana ranar jumma’a ta karshe na watan na Ramadan na ko wace shekara da ta zama ranar Qudus ta duniya, ranar da musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya zasu daga muryoyinsu da nunan goyinbayansu ga al-ummar kasar Palastinu wadanda ake zalanta. Jagoran juyin musuluncin ya kara da cewa, a cikin yan shekarun da suka gabata, kasashen yamma musamman Amurka da Ita HKI sun yi kokarin ganin sun mantar da al-ummar musulmi batun Palasdinu da kuma zaluncin da yahudawan Sahyoniyya suke musu, ta hanyar kokarin samar da sulhu, da kasashe biyu na al-ummu biyu ta Palasdinawa da kuma yahudawan sahyoniyya,
Amma habakar da raya ranar Qudsu take samu a ko wace shekara da kuma borin farkawar Musulunci wanda ya taso koma ya ci gaba da faruwa a kasashen musulmi da dama a yankin gabas ta tsakiya, ya sake farfado da baton kasar Palasdinu, ya kuma maida shi matasala mafi muhimmanci ga al-ummar musulmin a duka fadin duniya. An gudanar da zanga zangar ranar Qudsu ta duniya ne a ranar jumma’a da ta gabata a cikin kasashen duniya kimani 70, inda musulmi masu azumi suka daga muryoyinsu suka yi ta kira da aka kawo karshen mamayar kasar Palasdinu suka kuma yi tir da manya manyan kasashen duniya masu goyawa yahudawan sahyoniyya baya kan mamayar da suke wa kasar Palasdinawa. azzaluman shuwgabannin da suka shude, na su tabbatar da cewa sun waraware wadannan makirce makircen da makiya musulmi da Musulunci suke kullawa.
1084245