IQNA

Sarakunan Bahrain Ba Su Dauki Jinin Matasan kasar Da Kimar da Takai Gangar Mai Guda Ba

23:32 - August 26, 2012
Lambar Labari: 2399423
Bangaren kasa da kasa, jagoran mabiya tafarkin iyalan gidan amnzo a kasar bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa mahukuntan kasar ba su dauki jinin matasana kasar ad suek neman sauyi ta hanyar lumana a matsayi na koda gangar mai daya ba kamar yadda hakan yake samun goyon bayan kasashen larabawa da na turai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, jagoran mabiya tafarkin iyalan gidan amnzo a kasar bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa mahukuntan kasar ba su dauki jinin matasana kasar ad suek neman sauyi ta hanyar lumana a matsayi na koda gangar mai daya ba kamar yadda hakan yake samun goyon bayan kasashen larabawa da na turai da mahukuntan an bahrain suke yi musu biyayya kamar rakumi da akala.
masu neman sauyi a kasar Bahrain sun rufe dukkanin muhimman tituna da ke cikin kasar musamman masu isa birnin Manama fadar mulkin kasar inda suka hada duk wani kai komo domin tabbatar wa duniya cewa suna nan kan bakansu na neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar.
Mahukuntan kasar Bahrain sun kame daya daga cikin mambobin jam’iyyar adawa ta Amal Islami a ci gaba da daukar matakai na murkushe yunkurin da al’ummar kasar ke na neman gyara ta hanyar lumana.
Al’ummar kasar Bahrain sun fara gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ta gama gari a duk fadin kasar mai taken nasara ko kuma shahadada nufin tabbatar wa duniya cewa suna nan kan bakansu na neman hakkkokin su babu gudu ba ja da baya kan ahkkokinsu da aka haramata musu a matsayinsu na ‘yan kasa.
Dubban daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar kasar Bahrain a kasar Iraki, saboda tsabar zaluncin da suke fuskanta daga masarautar kama karya ta kasar, inda ake murkushe su da karfi tare da kame su da azabtar da su saboda sun nemi hakkokinsu na ‘yan kasa da aka haramta musu.
A kwanakin baya ne dai bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
1084203












captcha