IQNA

Mahnukuntan Wahabiyawan Saudiyya Sun Ci Zarafin Masu Ziyarar manzon Allah

23:31 - August 26, 2012
Lambar Labari: 2399424
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan Saudiyya sun ci zarafin wasu daga cikin masu ziyarar manzon Allah a birnin mdina mai alfarma saboda sun daga murya wajen yin salati ga manzon Allah da iyalan gidanmsa tsarkaka wanda hakan ya yi hannunriga da koyarwar akidar wahabiyanci da ke tsananin gaba da manzon Allah da iyalan gidansa.
Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa, yanakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mahukuntan Saudiyya sun ci zarafin wasu daga cikin masu ziyarar manzon Allah a birnin mdina mai alfarma saboda sun daga murya wajen yin salati ga manzon Allah da iyalan gidanmsa tsarkaka wanda hakan ya yi hannunriga da koyarwar akidar wahabiyanci da ke tsananin gaba da manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya Amnesty international ta yi kakkausar suka kan masarautar kasar Saudiyya ta gidan sarautar Al-saud da suke mulki a kasar kan danne hakkokin bil adama da suke yi a kasar musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah marassa rinjaye wadanda aka mayar da su saniyar ware a cikin harkokin kasar.
A wani batun kuma masana da dama sun amannar cewa ficewar dakarunnato daga kasar Libya shi ne kawai hanyar kawo karshen rikicin da kasar atke fama da shi tun bayan kisan gillar da suka yi wa tsohon jagoran kasar a lokacin da suka kaddamar da hari da sunan taimaka ma ‘yan tawaye wadanda daga bisani kuma suka gagare su.
Gwamnatocin kasashen lebanon da Libya sun cimma matasa dangane da makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa biyu ta hanyar kafa wani kwamiti da zai bi kadun wannan batu da ya hada dukaknin bangarorin biyu.
1084577
captcha