Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama, cewa an tattauna muhimman batutuwa da suka dangaci matsalolin da musulmin kasar Myanmar suke ciki tun bayan da mabiya addinin da kuma mahukuntan kasar suka fara yin kisan gilla a kansu kimanin watanni uku da suka gabata ba tare da wata kasa ta ce uffan ko daukar matakan da suka dace kan mahukuntan na Myanmar ba ta hanayar yanke alaka ko ladabtawar ta vtatalin arzki.
Ga dukkanin alamu'kisan da 'yan budda su ke yi wa musulmi a cikin Muyammar suna yi ne da tallafin gwamnatin kasar. Su ke kuma korarsu daga gidajensu da maida su zama 'yan gudun hijira na tilas. A tsammani shi ne addinin Budda wanda ya yi imani da halin kirki da kyautatawa halittu, da s u ke kira Neravana, su zama masu kyautatawa abokan zama da su. A lokacin da 'yan taliban su ka tarwatsa gumakan Budda a Afgahnistan , wadannan musulmin da ake kashe wa a yanzu sun yi Allah wadai da Taliban su ka kuma bayyana abinda su ka yi da cewa keta ce da mugunta.
Daruruwan shekaru musulmin kasar Thalidan su ka yi suna rayuwa da mabiya addinin Budda, amma ana samun sauyin siyaya a cikin kasar sai abokan zamansu su ka ci amanarsu da fara kashe su. Da gangan ake son nuna cewa a duk inda musulmi su ke a duniya masu son tada hankali ne. Wannan siyasa ce yammacin turai ke amfani da ita a lokaci mai tsawo. Wannan kuwa ba shi ne karon farko ba da aka yi wa musulmin mayammar kisan kiyashi. A tsawon lokacin mulkin sojan wannan kasa sun zama zakaran gwajin dafi na nuna kiyayya a gare su.
Abin da ake sa ran kungiyoyin kasa da kasa su aikata shi ne kawo karshen wannan irin kisan da ake yi wa musulmin muyammar, saboda su ma su rayu daidai da kowace al'umma a duniya. Idan a tsawon shekarun baya har zuwa 2010 gwamnarin Mayammar ta kasance a cikin killcewa daga kasashen duniya saboda mulkin soja na kama-karya, to shakka babu kisan kiyashin da ta ke yi wa musulmi zai maida ita zama mai laifi akalla a idon sauran musulmin duniya. Musamman ma dai kasashen musulmin kuda maso gabacin Asiya kamar su Indonesiya da Malasia da su ke a wannan yankin.
1084933