IQNA

Darul Ifta Na kasar Masar Ya Yi Allawadai da Rusa Kabrukan Bayin Allah A Libya

22:23 - August 29, 2012
Lambar Labari: 2401566
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar bayar ta fatawa ta kasar Masar ta yi kakkausar da yin Allawadai da rusa kbrukan waliyya da ‘yan salafiyya na kasar Libya suka yi wanda a cewar cibiyar hakan ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinin muslunci duk kuwa da cewa abin da ya fi muni shi ne masu aikata wannan mumman aiki suna yinsa da sunan addinin muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na gnet, cewa a jiya babbar cibiyar bayar ta fatawa ta kasar Masar ta yi kakkausar da yin Allawadai da rusa kbrukan waliyya da ‘yan salafiyya na kasar Libya suka yi wanda a cewar cibiyar hakan ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinin muslunci duk kuwa da cewa abin da ya fi muni shi ne masu aikata wannan mumman aiki suna yinsa da sunan addinin muslunci, da kuma jahilci.
Babban mai baiwa shugaban kasar Algeria shawarwari kan harkokin siyasa ya yi kakkausar suka kan kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da matakin da ta dauka kan rikicin kasar Syria.
Jaridar Damas Post ta kasar Syria ta habarta cewa, a zantawar da ta yi da babban mai baiwa shugaban Algeria shawara kan harkokin siyasa Abdulaziz Bilkhaddam ya bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta tafka babban kure dangane da matakin da ta auka kan rikicin kasar, inda take neman agaji daga kasashe makiyan larabawa da su taimaka mata domin kawo karshen gwamnatin Syria, y ace maimakon haka da ya kamata kungiyar kasashen larabawa ta taimaka wajen warware rikin ne ta hanyar dukkanin bangarori zuwa tattaunawa, ba goyon bayan 'yan adawar Syria da suke dauke da makamai ba.
Kungiyar kasashen larabawa tare da Amurka da Faransa da kuma Birtaniya har ma da haramtacciyar kasar Isra'ila ta bayan fage, sun hada kai domin ganin bayan shugaba Asad ko ta wace hanya, da hakan ya hada da baiwa 'yan bindigar kasar makamai da makudan kudade.
1086764

captcha