IQNA

Dole Ne A warware Matsalar Syria Ta Hanyar Tattaunawa Da Diplomasiyya

21:58 - August 31, 2012
Lambar Labari: 2402199
Bangaren kasa da kasa, dole ne a warware matsalolin da ake fama da su a kasar syria ta hanyar lumana da tattaunawa tsakanin bangarorin gwamnati da kuma yan adawa maimakon karfafa ayyukan ta’addanci domin tabbbatar da manufofin kasashen turai da yahudawan sahyuniya a cikin yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinajad ya bayyana cewa dole ne a warware matsalolin da ake fama da su a kasar syria ta hanyar lumana da tattaunawa tsakanin bangarorin gwamnati da kuma yan adawa maimakon karfafa ayyukan ta’addanci domin tabbbatar da manufofin kasashen turai da yahudawan sahyuniya a cikin yankin gabas ta tsakiya ta hanyar hyaddasa rikici.
Kasar Masar ta mika ragamar jagorancin kungiyar 'yan ba ruwanmu ta Non-Aligned Movemement wato NAM ga kasar Iran a yayin zaman babban taron kungiyar a yau alhamis. A bayan bude zaman babban taron shugabannin kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ta Non-Aligned Movement wato NAM karo na 16 a birnin Tehran na kasar Iran a yau alhamis; Shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya mika ragamar jagorancin kungiyar ga shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad a matsayin sabon shugaban kungiyar ta NAM karo na 16 bayan da wa'adin shugabancin Masar ya zo karshe.
A jawabin da ya gabatar bayan karbar jagorancin kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a yau alhamis: shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad ya bayyana cewa; Takaita ikon gudanar da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ga wasu tsirarun kasashe da suke dauke da ra'ayin jari hujja shi ne dalilin karfafa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan ci gaba da aiwatar da ayyukan zalunci.
Ahmadi Najad ya kara da cewar kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya mamaye matsayin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda kwamitin tsaron yake cin albasa da bakin babban zauren Majalisar, kuma babu wata 'yantacciyar kasa a duniya da ta isa ta koma ga kwamitin tsaron Majalisar ta Dinkin Duniya domin neman hakkinta.
Shugaban kasar Iran ya kuma jaddada cewar babu wani mataki da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya dauka kan matsalolin Palasdinawa, sai kara goyawa haramtacciyar kasar Isra'ila baya kan mamayar da take yi.
1088427






















captcha