IQNA

Amurka Da Haramtacciyyar Kasar Isra’ila Su Ne Musababbin Rikicin Syria

21:57 - August 31, 2012
Lambar Labari: 2402201
Bangaren siyasa, gwamnatin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila su ne ummul habaisin dukaknin matsalolin da al’ummomin duniya suke fama da su kamar yadda su ne suka sabbaba dukkanin rikicin da yake faruwa yanzu haka akasar Syria domin kawai su cimma manufofinsu an siyasa aynakin.
Kamfanin dilalncin labaran iqn ay habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagoran juyin juya hali cewa, a lokacin da yake ganawa da pira ministan kasar Syria, jagoran ya bayyana cewa gwamnatin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila su ne ummul habaisin dukaknin matsalolin da al’ummomin duniya suke fama da su kamar yadda su ne suka sabbaba dukkanin rikicin da yake faruwa yanzu haka akasar Syria domin kawai su cimma manufofinsu an siyasa aynakin gabs ta tsakiya baki daya.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Siriya ya bayyana furucin da shugaban kasar Masar ya yi kan Siriya a matsayin tsoma baki a harkokin da ya shafi kasar ta Siriya. Walid Mu'allim ministan harkokin wajen kasar Siriya ya bayyana cewar furucin da shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya yi kan kasar Siriya furuci ne da ya fice daga kan tsarin tafiyar kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM, inda ya shiga fagen tsoma baki a harkokin cikin gidan Siriya da take mamba a kungiyar 'yan ba ruwanmu.
Har ila yau ministan harkokin wajen kasar ta Siriya ya kuma bayyana kalaman da Mursi ya yi kan Siriya da cewa; kalamai ne da suke bayyana Muhammad Mursi a matsayin shugaban wata kungiya, ba shugaban kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM ba. A yau ne dai shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya yi suka kan gwamnatin Siriya a jawabin da ya gabatar a zaman taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a birnin Tehran na kasar Iran.
Mursi ya ambaci 'yan tawayen Siriya da suke dauke da makamai a matsayin 'yan gwagwarmaya, tare da siffanta gwamnatin Siriya a matsayin mai nuna fin karfi da kokarin murkushe al'umma, kamar yadda shugaban kasar ta Masar ya bayyana goyon bayan masu bijirewa gwamnatin Bashar Asad a matsayin wajibin da ya dace. 1088469
captcha