Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, shugaban Masar ya bayyana cewa bababn aikin da ke gaban kungiyar yan ba ruwanmu a halin yanzu shi ne mayar da hankali ga abubuwan da ke gabanta na yaki da nuna banbanci tsakanin al’ummomi da kuma yaki da ta’addanci a fadin duniya a matasayi na kasa domin duniya ta samu zaman lafiya daga ayyukan ta’addanci.
Dangane da maganganun batunci da shugaban kasar Masar ya yi a gaban taron kuwa ministan harkokin wajen kasar Siriya ya bayyana furucin da shugaban kasar Masar ya yi kan Siriya a matsayin tsoma baki a harkokin da ya shafi kasar ta Siriya. Walid Mu'allim ministan harkokin wajen kasar Siriya ya bayyana cewar furucin da shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya yi kan kasar Siriya furuci ne da ya fice daga kan tsarin tafiyar kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM, inda ya shiga fagen tsoma baki a harkokin cikin gidan Siriya da take mamba a kungiyar 'yan ba ruwanmu.
Har ila yau ministan harkokin wajen kasar ta Siriya ya kuma bayyana kalaman da Mursi ya yi kan Siriya da cewa; kalamai ne da suke bayyana Muhammad Mursi a matsayin shugaban wata kungiya, ba shugaban kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM ba. A yau ne dai shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya yi suka kan gwamnatin Siriya a jawabin da ya gabatar a zaman taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a birnin Tehran na kasar Iran.
Mursi ya ambaci 'yan tawayen Siriya da suke dauke da makamai a matsayin 'yan gwagwarmaya, tare da siffanta gwamnatin Siriya a matsayin mai nuna fin karfi da kokarin murkushe al'umma, kamar yadda shugaban kasar ta Masar ya bayyana goyon bayan masu bijirewa gwamnatin Bashar Asad a matsayin wajibin da ya dace su yi hakan, ba tare da ambaton ayyukan ta’addancin da suke yi ba. 1088131