IQNA

Bayanin Bayan Taron Birnin Tehran Ya Mayar Da Hankali Kan Batun Palastinu

21:50 - September 01, 2012
Lambar Labari: 2402803
Bangaren siyasa, bayanin bayan taron kasashen yan ba ruwanmu da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran ya yi ishara da muhimmancin kawo karshen mamayar da ake yi wa al’aummar palastinu da kuma dukaknin palastinawa damar zabar makomarsu da kansu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na cikin gida cewa, bayanin bayan taron kasashen yan ba ruwanmu da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran ya yi ishara da muhimmancin kawo karshen mamayar da ake yi wa al’aummar palastinu da kuma dukaknin palastinawa damar zabar makomarsu da kansu na ciki da wadfanda ke gudun hijira.
Jawabin bayan taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta Non-Aligned Movement wato NAM karo na 16 da aka gudanar a kasar Iran ya samu amincewar dukkanin mahalarta zaman taron. Shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad a matsayinsa na sabon shugaban kungiyar ta 'yan ba ruwanmu wato NAM ya karanta jawabin bayan taron kungiyar a jiya juma'a da dare, inda bayanin bayan taron ya kunshi nuna cikekken goyon baya ga shirin makamashin nukiliyar kasar Iran, adawa da bakar siyasar Amurka na kakaba takunkumin bangare guda kan kasar Iran da yin kira ga kara matsa kaimi wajen nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu.
Har ila yau jawabin bayan taron na kungiyar NAM ya bukaci daukan matakin yaki da bata sunan addinin Musulunci da nuna wariya a duk fadin duniya, kamar yadda ya jaddada daukan matakan raba duniya da makaman nukiliya, tare da jaddada goyon baya ga mallakar fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya don bunkasa ci gaban kasa.
A karshen zaman taron a jiya juma'a shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad ya bayyana zaman taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM karo na 16 a matsayin mai tasiri da ya shiga cikin kundin tarihi, tare da jaddada cewa; zaman taron yana dauke da muhimmin sako ga dukkanin kasashen duniya, sannan ya jinjinawa dukkanin mahalarta zaman taron.
A ranar lahadin da ta gabata ce dai aka bude zaman taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a birnin Tehran na kasar Iran karo na 16, inda zaman taron ya samu halartar wakilan kasashe fiye da 100 na duniya tare da kungiyoyin kasa da kasa ciki har da Majalisar Dinkin Duniya.
1088704






















captcha