IQNA

Jamhuriyar Muslunci Ta Kama hanyar Aiwatar Da Manufofinta Da Gaske

21:50 - September 01, 2012
Lambar Labari: 2402804
Bangaren siyasa, a zantawar da ya yi da shugaban majalisar dokokin kasar korea ta arewa jagoran juyin juya halin muslunci ya jaddada cewa kasar Iran a shirye take ta ci gaba da aiwatar da manufofinta ba tare da ja da baya ba ko jin tsoron abin ka iya kai ya komo domin kuwa hadafi shi ne manufa ba abubuwan da suke zama hanya zuwa gare shi ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafin jagora cewa, a zantawar da ya yi da shugaban majalisar dokokin kasar korea ta arewa jagoran juyin juya halin muslunci ya jaddada cewa kasar Iran a shirye take ta ci gaba da aiwatar da manufofinta ba tare da ja da baya ba ko jin tsoron abin ka iya kai ya komo domin kuwa hadafi shi ne manufa ba abubuwan da suke zama hanya zuwa gare shi ba kamar yadda wasu suke zato.
A daya bangare guda kuma Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullahil-Uzmah Sayyed Ali Khamenei ya bayyana cewa ko shakka babu Amurka da kuma gwamnatin mamaya ta Isra'ila ne ke rura wutar rikicin da ke faruwa a kasar Siriya. Jogoran ya kuwa bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Firayi Ministan kasar Siriya Wa'el Nader Alhalqi, wanda ke halartar taron kungiyar 'yan ba Ruwanmu a nan birnin Tehran.
Jagaoan ya yi gargadin cewa matukar dai aka ci gaba da zura ido Amurka da kuma Yahudawan Sahyuniyya suak ci gaba da bai wa 'yan ta'addar kasar Siriya makamai da kuma kudade, to lalle kuwa abin da zai faru ga kasashen wannan yanki zai iya kasancewa babban bala'I a nan gaba, saboda haka ya bukaci da a gaggauta dakatar da hakan domin hana kara tsunduma wannan yankin a cikin wasu matsaloli.
A gefen taron na kungiyar 'yan baruwanmu da ke gudana a nan birnin Tehran, a yau juma'a jagoran na juyin juya halin musulunci na Iran ya gana da shuwagabannin kasashen duniya da dama da ke halartar taron, da suka hada da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, da na kasar Labanan Mishel Suleiman, da shugaban kasar Sri Lanka Mahinda Rajapaska.
Har ila yau jagoran na juyin musulunci a yau ya gana da shugaban kasar Pakistan Asif Zardari, da shugaban Sudan Umar Hasan Albashir da kuma shugaban Majalisar Dokokin kasar Aljeriya Abdulkadir Ben Saleh.
1089010
captcha