Bangaren siaysa, ya zama kan dukkanin kasashe mambobi a kungiyar kasashen yan ba ruwanmu su mayar da hankali wajen daukar bmatakai da suka dace domin kawo karshen zaluncin manyan kasashen duniya kan sauran kasashe masu rauni wanda kuma hakan ba zxai kasance ba har sai idan wadannan kasashe su ci gaba da hada kansu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa jagoran juyin juya hali ya jaddada cewa ya zama kan dukkanin kasashe mambobi a kungiyar kasashen yan ba ruwanmu su mayar da hankali wajen daukar bmatakai da suka dace domin kawo karshen zaluncin manyan kasashen duniya kan sauran kasashe masu rauni wanda kuma hakan ba zxai kasance ba har sai idan wadannan kasashe su ci gaba da hada kansu wanda shi ne mabudin nasara.
Shi kuwa a nasa bangaren Shugaban kasar Iran ya jaddada wajabcin aiwatar da gyare-gyare a tsarin tafiyar da duniya, tare da daukan matakin kalubalantar bakar siyasar hadama da babakere. A jawabin da ya gabatar a yayin bikin rufe zaman babban taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM karo na 16 da aka gudanar a birnin Tehran na kasar Iran a jiya juma'a; shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad ya bayyana wajabcin kare mutuncin bil-Adama da hakkokinsa, kare dokokin Ubangiji mahalicci, wanzar da adalci, samun tsarkin zuciya da watsuwar aminci da soyayya a duniya.
Har ila yau Ahmadi Najad ya jaddada cewa dole ne a kara samun bunkasar dankon zumunci da 'yan uwantaka a tsakanin mambobin kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM, gami da tsayin daka da yin riko da manufofin kungiyar domin kalubalantar bakar siyasar hadama, babakere da son rai da ke addabar duniya. Shugaba kasar ta Iran ya kara tunasar da mahalarta zaman taron na kungiyar NAM muhimmancin yin watsi da siyasar kunna wutan rikici da tashe tashen hankula a duniya, tare da kwadaitar da su wajabcin yin riko da matakan hankali wajen warware matsalolin da suke addabar duniya da nufin wanzar da adalci da aminci.
1089005