Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews, cewa mabiya addinin muslunci sun fara gudanar da zamansu na shekara a birnin Washinton fadar mulkin kasar wanda shi ne karo na arba’in da tara da suke gudanar da wannan taro domin tattauna matsalolinsu da kuma abubuwan da ske bukata sukai gaba domin tabbabat da bin hakkokinsu na yan kasa da ake danne musu.
A bangare guda kuma wani bayanin ya ce gwamnatin Syria ta aike da wasu wasiku biyu zuwa ga babban sakataren majalisar dinkin duniya da kuma shugaban kwamitin tsaron majalisar, dangane da karuwar ayyukan ta'addanci bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
A cikin wasikun biyu, gwamnatin Syria ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta safke nauyin da ya rataya a kanta, wajen matsa lamba kan gwamnatocin da suke taimaka ma ayyukan ta'addanci a cikin kasar Syria, ta hanyar baiwa 'yan bindiga makamai da makudan kudade, domin kuwa a cewar bayanin, idan har gwamnatin Syria za ta amince da wannan yarjejeniya da kuma yin aiki da ita, babu dalilin da zai sanya a bar daya bangaren rikicin yana cin karensa babu babbaka.
Bayanin ya ce tawagogi na masu sanya ido na kasashen larabnawa da majalisar dinkin duniya sun gane wa idanunsu hakikanin abin da ke faruwa a kasar, saboda haka kawo karshen tashin hankali a kasar ya doru ne kan dakatar da kasashen masu taimaka ma ayyukan ta'addanci, musamman ma na larabawa daga cikinsu, wadanda suka sanar da hakan a hukumance.
1088860