Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na geotribune, cewa kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta fitar da wani bayani da acikinsa ta kore dukaknin bayanan shirme da wata kungiyar yan salafiyya da ke da dangataka da gwamnatin wahabiyawan Saudiyya ta fada da ke cewa kungiyar ta hizbullah ce ta yi sanadiyyar raguwar yawan masu shakatawa a kasar.
Dangane da abin da yake faruwa a kasar Syria kuwa, da kuma wajabcin kawo karshensa ta hanyoyi na lumana, wanda daya ne daga cikin kudurori bakawai da bayanin bayan taron ya kunsa, hakika mun yi imanin cewa kowace irin matsala za a iya warware ta ne kawai ta hanyar komaw akan teburin tattaunawa tsakanin dukaknin bangarorin siyasar kasar tare da gwamnati, bin duk wata hanya sabanin hakan zai kara iza wutar rikicin ne kawai, saboda haka muna fatan ganin bangarorin rikicin Syria sun ajiye sabanin da ke tsakaninsu gefe guda, sun koma ga tattaunawa da junansu nan ba da jimawa, domin kasar ta samu komawa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda take kafin rikicin.
Dangane da gudanar da wannan taro a kasar Iran kuwa amar yadda babban sakataren MDD ya fada, Iran na daga cikin mambobin wannan kungiya da suke taka rawar gani yankin gabas ta tsakiya, kuma a halin yanzu shugaban kasar Iran shi ne ya karbi jagorancin wannan kungiya a wajen wannan taro da aka gudanar a nan birnin Tehran, saboda haka muna jinjinawa da yabawa matuka ga jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da yadda ta karbi bakuncin wannan taro da ya samu halartar wakilan kasashe 120 mambobin kungiyar, da suka haka da shugabannin kasashe da kuma mataimakan shugabanni gami pira ministoci da ministocin harkokin waje, da kuma wakilan kungiyoyi na kasa da kasa da suka hada da MDD, kuma ba mu da shakku kan cewa Iran za ta yi iyakacin kokarinta domin ganin cewa abubuwan da kungiyar ta sanya a gaba sun cimma nasara, domin ayyukan kungiyar NAM ayyuka ne hadin gwiwa da taimaka ma juna, wanda kuma ko shakka babu sauran kasashe kamar Nigeria za su kasance tare da Iran domin tabbatar da nasarar ayyukan wannan kungiya.
1088801