Bangaren kasa da kasa, babu wani tabbaci kan makomar Imam Musa Sadr tun bayan sace kuma a halin yanzu gudanar da bincike kan makomar Imam Muysa Sadr yana daga cikin muhimman lamurra da gwamnatin kasar Lebanon ta mayar da hankali kansu a halin yanzu tare da abokian tafiyarsa biyu wadanda suka bata a kasar Libya tun bayan da tsohon shugaban kasar ya gayyace su a matsayin bakinsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa shugaban majalisar dokokin Lebanon Nabih Birri ya sheda cewa babu wani tabbaci kan makomar Imam Musa Sadr tun bayan sace kuma a halin yanzu gudanar da bincike kan makomar Imam Muysa Sadr yana daga cikin muhimman lamurra da gwamnatin kasar Lebanon ta mayar da hankali kansu a halin yanzu tare da abokian tafiyarsa biyu wadanda suka bata a kasar Libya tun bayan da tsohon shugaban kasar ya gayyace su a matsayin bakinsa kuma ya batar da su.
Yan Salafiyya da ke mamaye da yankunan Arewacin kasar Mali, a jiya asabar sun kutsa tare kuma da kwace garin Douentza da ke cikin lardin Mopti na Kudancin kasar, wanda kuma shi ne karo na farko da mayakan masu ra'ayin Islama suka kama wani yanki da ke Kudancin kasar ta Mali. Rahotanni sun ce da misalin karfe 8 na safiyar jiya agogon kasar ta Mali ne, mayakan Kungiyar Mujao wato daya daga cikin kungiyoyin 'yan Sallafiya da ke mamaye da Arewacin kasar suka yi wa garin na Douentza kawanya kofar-rago, inda kuma suka bukaci mayakan sa-kai da ke garin da ake kira da suna ''Ganda-Izo'' da su mika makansu,
Bayan sun kwance masu damara ne kuma suka kore su daga garin. Wani mazauni garin mai suna Almahdi Cisse, ya ce tuni mayakan na Mujao suka kama karamin barikin sojan da ke birnin tare kuma da dora tutarsu a kan wasu gine-gine da ofisoshin hukuma domin tabbatar da ikonsu a garin. Kafin birnin na Douentza, tun a cikin watan Maris da ya gabata kungiyoyin na 'yan Salafiyyar ne ke rike da garuruwan Tumbuktu, Gao da kuma Kidal da ke Arewacin kasar.
1088761