IQNA

Gasar Kur’ani Babbar Dama Ta samun Gagarumin Hadin kai Tsakanin Musulmi

17:57 - September 02, 2012
Lambar Labari: 2403547
Bangaren kasa da kasa, Imam Sadiq (AS) bababn gishiki ne na gina tunanin dan adam kan sahihin tafarki da zai kais hi bin Allah madaukakin sarki daidai da abin da yake acikin addini kamar dai yadda daya daga cikin malaman addinin Musulunci daga bangaren yan sunna ya sanar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a Iraki, cewa Imam Sadiq (AS) bababn gishiki ne na gina tunanin dan adam kan sahihin tafarki da zai kais hi bin Allah madaukakin sarki daidai da abin da yake acikin addini kamar dai yadda daya daga cikin malaman addinin Musulunci daga bangaren yan sunna ya sanar a cikin hudubar juma’a da ya gabata a wannan mako.
Ayoyi masu albarka sun yi bayani kan tsarin da duniya take tafiya a kansa wanda ya tabbatar da samuwar Allah ubangiji guda daya da ya halicci duniya da abin da ke cikinta, kuma yake tafiyar da su da ikonsa maras iyaka, tare da tabbatar da cewa da akwai wani ubangiji na daban abokin tarayya ga Allah madaukakin sarki, da tsarin duniya da ma dukaknin abin halitta ya rushe baki daya, saboda bat sari guda ne zai tafiyar da su ba.
Haka ita ma wannan aya mai albarka tana yin ishara da cewa, dukkanin annabawan da Allah madaukakin sarki ya aiko a zamunnan da suka gabata kafin ma’aiki (SAW) an aiko su ne domin su sheda ma mutane cewa babu wani abin bauta da gaskiya face Allah madaukakin sarki shi kadai, shi ne mahaliccin kowa da komai, shi ne mai kwararo samuwa ga dukkanin abin da ya halitta a cikin sammai da kassai, shi ne yake tafiyar da su bisa nufinsa ba tare da taimakon wani ba, a lokaci guda kuma shi ne masani bisa halin da halttunsa suke ciki, shi kuma ya cancanci bauta daga bayinsa.
Imam Ali (AS) ya ce da dansa Imam Hassan (AS) cewa: Ya dana, idan da akwai wasu alloli na daban koma bayan Allah madaukakin sarki, to da su ma sun aiko da nasu annabawan zuwa ga sauran mutane domin su sanar da su wadannan alloli, da kuma dokokinsu da ka’idojin da suke son dan adam ya rayu a kansu.


1070662












captcha