Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Morocco sun hana gudanar da taron jam’aiyyar msulunci ta kasar wanda yake kira zuwa ga nemnan sauyi da samar da adalci a tsakanin al’ummar kasar da kuma daina bauta ma sarki kamar yadda yake a cikin al’adun kasar tsawon shekaru.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa mahukuntan kasar Morocco sun hana gudanar da taron jam’aiyyar msulunci ta kasar wanda yake kira zuwa ga nemnan sauyi da samar da adalci a tsakanin al’ummar kasar da kuma daina bauta ma sarki kamar yadda yake a cikin al’adun kasar tsawon shekaru duk da cewa haklan ba demokradiyya ba ce.
Al’ummar palastinu jigo ne mai matukar muhimmanci a cikin dukaknin lamurra da suka danganci fadakar da al’ummar musulmi ta yi a wannan zamani musamman ma ganin cewa ita al’umma ce da ta farka tun shekaru da dama da suka gabata tana gwagwarmayar neman ‘yancinta da hakkokinta daga haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.
A nata bangaren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
1089552