Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na VIBE, cewa a jiya an nuna wani littafi mai suna Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a wani baje koli na Musulunci a kasar Jamus da nufin kara fito da matsayin muslunci da kuma bayyana abinda yake koyar da dan adam ta hanyar sakon da manzon tsira ya zo da shi daga Allah madaukakin sarki wato alkur’ani, wanda shi wannan manzon mai tsarki shi ne mai nuna yadda ake aiki da kur’ani.
Bnagare guda kuma jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee, ya jaddada muhimmancin ranar Qudus ta duniya ga mutanen kasar Iran da kuma sauran al-ummar musulmin duniya. Jagoran ya bayyana haka ne a jiya lahadi a cikin khudubobinsa na sallar idi wacce a aka gudanar a masallacin jumma’a ta Jami’ar Tehran a nan birnin Tehran. Jagoran ya yaba da yadda aka gudanar da zanga zangar ranar ta Qudus a nan kasar Iran da kuma wasu kasashen duniya a ranar jumma’a da ta gabata, jumma’a ta karshe na watan Ramadan.
Fiye da shekaru 30 da suka gabata ne Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ayyana ranar jumma’a ta karshe na watan na Ramadan na ko wace shekara da ta zama ranar Qudus ta duniya, ranar da musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya zasu daga muryoyinsu da nunan goyinbayansu ga al-ummar kasar Palastinu wadanda ake zalanta. Jagoran juyin musuluncin ya kara da cewa, a cikin yan shekarun da suka gabata, kasashen yamma musamman Amurka da Ita HKI sun yi kokarin ganin sun mantar da al-ummar musulmi batun Palasdinu da kuma zaluncin da yahudawan Sahyoniyya suke musu, ta hanyar kokarin samar da sulhu, da kasashe biyu na al-ummu biyu ta Palasdinawa da kuma yahudawan sahyoniyya,
Amma habakar da raya ranar Qudsu take samu a ko wace shekara da kuma borin farkawar Musulunci wanda ya taso koma ya ci gaba da faruwa a kasashen musulmi da dama a yankin gabas ta tsakiya, ya sake farfado da baton kasar Palasdinu, ya kuma maida shi matasala mafi muhimmanci ga al-ummar musulmin a duka fadin duniya. An gudanar da zanga zangar ranar Qudsu ta duniya ne a ranar jumma’a da ta gabata a cikin kasashen duniya kimani 70, inda musulmi masu azumi suka daga muryoyinsu suka yi ta kira da aka kawo karshen mamayar kasar Palasdinu suka kuma yi tir da manya manyan kasashen duniya masu goyawa yahudawan sahyoniyya baya kan mamayar da suke wa kasar Palasdinawa.
A wani bangare na jamwabinsa jagoran juyin Musulunci, ya yaba da yadda sauran musulmi a wasu kasashen duniya suka kara shigowa don raya wannan rana, don ganin al-ummar Palasdinu sun fita cikin halin da suke ciki na zalunci. Jagoran ya kara jaddada cewa, tafarki da kuma matakan da al-ummar musulmi a yankin gabas ta tsakiya suka dauka, tafarkin ne da ya dashe kuma ya bukace su da su ci gaba da ita. Ya kuma yi kira a garesu, da su yi hattara da makirci makircen makiya, musamman na kokarin jefa gaba da kiyyaya tsakanin al-ummar musulmi da nufin raba kansu, da kuma kauda su kan tafarkin da suke kai a halin yanzu.
Yay i kira ga shuwagabannin gwamnatocin kasashen musulmi, musamman wadanda suka maye gurbin azzaluman shuwgabannin da suka shude, na su tabbatar da cewa sun waraware wadannan makirce makircen da makiya musulmi da Musulunci suke kullawa.
1089631