Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa wasu daga cikin masana sun imanin cewa irin gogayyar da jamhuriyar muslunci ta Iran take da ita abangarori da dama hakan ya bata damar taka gagarumar rawa a bangarori da dama da hakan ya hada da batun Palastinu wanda ya zama babbar mahada da ta hada dukanin musulmi domin kuwa idan ana maganar palastinu ana batun masallacin Qods ne mai malfarma wanda ya hada dukaknin musulmi baki daya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa an gudanar da taron kungiyar yan ba ruwammu a nan Tehran a makon da ya gabata cikin tsari mafi kyau, wanda ya sami yabon manya manyan baki da kuma shuwagabannin kasashen da suka halarci taron. Salihi ya bayyana haka ne a jiya da yamma a wani hira ta musamman wanda gidan Television Chanel Two na nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran yay i da shi.
Salihi ya kara da cewa wani abu da ya kebance taron kungiyar yan ba ruwammu karo na 16 a nan Tehran shi ne amincewa da dukkan shawarorin da aka tattauna a kansu a cikin taron ba tare da ja in ja ba. Har’ila yau taron ya nuna da cewa gwamnatin Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta yi nasara a kan kasashen yamma wadanda suke son ganin kasashen duniya sun maida ita saniyar ware.
Inji shi. Ministan ya kara da cewa kasancewar kasar Iran ce kasa wacce tafi zama yar ba ruwammu da bin manya manyan kasashen duniya na yamma ko na gabas, wannan ya sanya kasashen kungiyar suka sami karfin guiwan cewa kasar Iran zata iya yin tsiri mai amfani ga kungiyar. A lokacin taron na kimani mako guda, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da bakin taron 16, wadanda suka hada da babban sakataren MDD Banki Moon, Priministan kasar India Manmonhang Sing, da kuma sauransu.
Sai kuma shugaba kasar Iran Dr Mahmood Ahmadi Najada wanda ya gana da manya manayan baki 15, wadanda suka hada da shugaban kasar Masar Muhammad Muri da . Salihi ya ce shi kadai ya gana da ministocin harkokin wajen kasashe 63 na kasashen kungiyar da suka halarci taron.
1090584