Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu dangane da mu’ujizar kur’ani mai tsarki wanda ya samu halartar malamai da kuma matasa daga sassan kasar domin amfana da muhimman bayaai da ake gudanarwa a wurin da kuma makamalolin da aka raba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CTME, cewa a jiya a na gudanar da wani zaman taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu dangane da mu’ujizar kur’ani mai tsarki wanda ya samu halartar malamai da kuma matasa daga sassan kasar domin amfana da muhimman bayaai da ake gudanarwa a wurin da kuma makamalolin da aka raba domin amfanin mahalarta.
Babbar jam'iyyar adawa ta tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ta jaddada wajabcin ci gaba da gudanar da shirin wanzar da sulhu da hadin kan kasa a Ivory Coast. A jiya talata ce manyan jami'an jam'iyyar adawa ta FPI ta tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo da manyan wakilan jam'iyya mai mulki a kasar ta RDR suka gudanar da zaman tattaunawa kan batun ci gaba da gudanar da shirin wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar, tare da jaddada goyon bayansu ga shirin.
A yayin zaman taron Amadou Soumahoro babban sakataren jam'iyyar da ke mulki a kasar ta Ivory Coast ya bukaci dukkanin kungiyoyi da jam'iyyun siyasa da su mutunta gwamnati da mahukuntan kasar don basu damar gudanar da mulkin kasa cikin aminci. A nashi bangaren kakakin jam'iyyar adawa ta FPI Sebastien Dano Djedje ya jaddada matsayin jam'iyyarsa na rashin amincewa da duk wani tashin hankali da rikici a kasar Ivory Coast, tare da jaddada wajabcin ci gaba da gudanar da zaman tattaunawa don warware matsalolin da suke addabar kasar.
1090667