IQNA

Mazhabar Iyalan Gidan Manzo Ta Samu Karbuwa A Indonesia Bayan Juyin Iran

22:17 - September 05, 2012
Lambar Labari: 2406059
Bangaren kasa da kasa, mazhabar iayaln gidan amnzo ta samu karbuwa ne da bunkasa a kasar Indonesia bayan juyin juya halin muslunci da ak ayi kasar Iran shekaru kimanin talatin da uku da suka gabata sakamakon isar da sakon da ake yi ta hanyar malamai da dama da suke aikin tabligi.
Kamfanindillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa daya daga cikin mabiya tafarkin manzo daga kasar Indonesia ya bayyana cewa mazhabar iayaln gidan amnzo ta samu karbuwa ne da bunkasa a kasar Indonesia bayan juyin juya halin muslunci da ak ayi kasar Iran shekaru kimanin talatin da uku da suka gabata sakamakon isar da sakon da ake yi ta hanyar malamai da dama da suke aikin tabligin sakon addini.
A wani labarin kuma Ramin Mehmanparast kakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa samun cikakkiyar hulda tsakanin marubuta na kasashen musulmi hakan zai taimaka matuka wajen fitar muhimman lamurra da musulmi suke yin rubutu a knsu na addini domin amfanin sauran mutanen duniya, musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.
Ya ce a koda yaushe marubuta suna taka gagarumar rawa wajen fitar da kowane irin lamari ga sauran mutane, inda sukan yi amfani da hikimar da Allah ya basu wajen ganin sun isar da sako cikin sauki zuwa ga kwakwalwar mai karatu, wanda kuma idan marubuta daga cikin marubutan musulmi suka samu wata kyakyawar dangantaka ko shakka babu hakan zai ba su damar isa da sakon addini da munufofinsa ga sauran al’ummomi.
Mehman paranst kakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa samun cikakkiyar hulda tsakanin marubuta na kasashen musulmi hakan zai taimaka matuka wajen fitar muhimman lamurra da musulmi suke yin rubutu a knsu na addini domin amfanin sauran mutane na duniya baki daya.
1091052



















captcha