IQNA

Mabiya Tafarkin Iayalan Gidan Na Jiran Samun Labari Dangane Da Imam Musa Sadr

11:14 - September 10, 2012
Lambar Labari: 2408679
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzo na jiran samun labara dangane da makomar Imam Musa Sadr wanda ya bata akasar Libya tun kimanin shrekaru talatin da biyar da suka gabata bayan gayyatar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya aike masa da ita.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa mabiya tafarkin iyalan gidan manzo na jiran samun labara dangane da makomar Imam Musa Sadr wanda ya bata akasar Libya tun kimanin shrekaru talatin da biyar da suka gabata bayan gayyatar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya aike masa da ita tare da abokan tafiyarsa biyu.
A wani labarin kuma yau asabar 'yan uwa da kuma makusanta wadanda suka rasa rayukansu ko kuma suka samu raunuka a lokacin boren da ya yi sanadiyyar kawar da shugaban kasar Tunisiya daga karagar mulki a cikin shekarar bara sun mamaye ofisoshin ginin gwamnan lardin Kasserine da ke Yammacin kasar. Shaidun gani da ido sun ce masu gudanar da tarzoma wadanda yawansu ya doshi dari daya, sun kutsa a cikin ofishin gwamnan inda kuma suka ce ba za fice daga cikinsa ba sai an samar masu da ayyukan yi, kuma tuni 23 daga cikinsu suka soma yajin kin cin abinci.
Haka zalika mutanen sun bukaci da a canza gwamnan lardin wanda ya foot daga jam'iyyar Ennahda da ke mulkin kasar ta Tunisiya, wata sanarwa da suka fitar a tsakiyar ranar yau, hukumomin kasar ta Tunisiya sun ce tuni suka kafa wani kwamiti da ke ci gaba da gudanar da ayyukansa, kuma ko shakka babu kwamitin ne zai gabatar da sunayen dukkanin wadanda suka samu raunuka da kuma 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon tarzomar da ta kawar da shugaba Zainal Abidin Ben Ali daga karagar mulki domin ba su ayyukan yi a cikin ma'aikatun kasar.
1094376





captcha