IQNA

Zaman Taro Dangane Da Cin Zarafin Dan Adam Da Ake Yi A Kurkukun Bahrain

11:13 - September 10, 2012
Lambar Labari: 2408680
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zama domin tatatuna muhimman batutuwa da suka danganci cin zarafin dan adam da ake yi a cikin gidajen kurku na kasar Bahrain wanda hakan yay i hannun riga da dukaknin kaidoji da dokoki na kasa da kasa duk kuwa da irin gagarumin goyon bayan da gwamnatin kasar take samu daga turawa domin hakan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani zama domin tatatuna muhimman batutuwa da suka danganci cin zarafin dan adam da ake yi a cikin gidajen kurku na kasar Bahrain wanda hakan yay i hannun riga da dukaknin kaidoji da dokoki na kasa da kasa duk kuwa da irin gagarumin goyon bayan da gwamnatin kasar take samu daga turawa domin hakan abin da ake ganin ya sabawa abin turawan suke rayawa na kare hakkin dan adam.
Jami'an tsaron kasar Masar sun yi dauki ba dadi da wasu gangun jama'a da suke goyon bayan 'yan tawayen kasar Siriya a birnin Alkahira a jiya talata. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarto daga wani jami'in tsaro cewa: A jiya Talata wasu gungun jama'a da suke da'awar kare hakkin bil-Adama sun yi kokarin kutsa kai cikin ofishin jakadancin kasar Siriya da ke birnin Alkahira da nufin daga tutar 'yan tawayen Siriya maimakon na gwamnatin kasar, don haka jami'an 'yan sanda suka taka musu burki, lamarin da ya janyo dauki ba dadi da har ya kai ga samun raunuka a tsakanin bangarorin biyu.
Tare da kame wasu mutane biyar daga cikin gungun jama'ar. Tun a cikin watan Maris na shekara ta 2011 ce yunkurin neman aiwatar da gyara a fuskar siyasar kasar Siriya ya kunno kai, amma kasar Amurka da kawayenta na kasashen yamma gami da 'yan koransu na kasashen Larabawa musamman Saudiyya da Qatar da kuma Turkiyya da ke makobtaka da Siriya suka dauki matakin samar da 'yan ta'adda tare da mallaka musu makamai da nufin kawar da gwamnatin Bashar Asad saboda matsayinsa na bijirewa bakar siyasar yammacin Turai da goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya, lamarin da ya wurga kasar ta Siriya cikin rikici da rashin zaman lafiya.
1094390


captcha