Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na levif, cewa an sanar cewa nan ba da jimawa ba za a yanke hukunci kan mutumin da ya kai hari kan masallacin Imam Rida (AS) da ke birnin Brussel na kasar Belgium bayan da likitan da ke duba lafiyarsa ta bangaren hankali ya tabbatar da cewa kutumin lafiyarsa lau ba shi da wata matsala ta rashin hankali kamar yadda aka yi zato.
A wani labarin kuma jam’iyyar adawa mafi girma akasar Bahrain ta Alwifaq ta bayyana cewa ba za ta taba amincewa da shirin da Amurka take da shi ba na rusa kasar Bahrain ta hanyarv yin amfani da wasu karnukanta da ke yankin domin mayar da kasar wani bangare na wata kasa daga cikin kasashen larabawa da ke aiwatar da siyasar Amurka da yahudawa a yankin.
Sheikh Isa Kasim babban malamin addinin muslunci kuma limamin kasar Bahrain ya bayyana cewa mahukuntan kasar manyan makaryatane domin kuwa suna bayyana ma duniya wani abu daban sabanin abin da suke aikatawa na ta’addanci da zalunci kan al’ummar kasar marassa kriya.
Daya daga cikin membobin kungiyar 'yan jaridar kasashen larabawa a Amurka ya zargi wasu kasashen larabawa da na yammaci da kaddamar da gagarumin yakin jirkitar hakikanin abin da ke faruwa a kasar Siriya don cimma manufar da suka sa a gaba kan kasar.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Press mai watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran cikin harshen turanci, Rafik Lutf memba a kungiyar 'yan jaridar kasashen larabawa a Amurkan ya ce tashar talabijin din nan ta Amurka da Al-Jazeera ta kasar da sauran wasu tashohin kasashen larabawan su ne kan gaba wajen jirkita hakikanin abin da ke gudana a kasar Siriya da kuma zargin gwamnati da kashe fararen hula alhali hakan aiki ne na 'yan ta'addan da suke samun makamai daga wajen wadannan kasashen.
1096514