Bnagaren kasa da kasa, a cikin wani furuci na rashin kunya daga shugaban alkaida Aiuman Zawahiri ya bayyan acewa kawar da shugaban kasar Syria Bashar Asad zai gaggauta kawo karshen haramtacciyar kasar Isra’ila saboda haka ya kirayi musulmi da su taimaka ma ‘yan ta’addan kasar ad su gaba da abin da suke yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shfain sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi ta kasar Masar cewa, a cikin wani furuci na rashin kunya daga shugaban alkaida Aiuman Zawahiri ya bayyan acewa kawar da shugaban kasar Syria Bashar Asad zai gaggauta kawo karshen haramtacciyar kasar Isra’ila saboda haka ya kirayi musulmi da su taimaka ma ‘yan ta’addan kasar ad su gaba da abin da suke yi na ta’addanci.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta shiga cikin jerin kasashen da suka haramta kayyakin haramtacciyar kasar Isra’ila kamar yadda wasu kasashe suka dauki irin wannan matakin tun da jimawa domin nuna rashin amincewarsu da zaluncin da take yi kan al’ummar palastinu marassa kariya kamar dai yadda yhaudawan sahyuniya suka shahara da hakan.
An shirya kara da za agabatar a gaban shari’a kan wasu yahudawan sahyuniya masu wulakanta kur’ani mai tsarki a cikin yankunan palastinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye domin tabbatar musu da cewa musulmi ba za su amince da abin da uke yi ba na keta alfarma kur’ani da sauran ababe masu alfarma a cikin addinin muslunci.
A bangare guda kuma a ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
1097650