IQNA

ISESCO Ta Yi Allawadai Da Cin zarafin Muslunci Da Amurkawa Suke Yi

23:42 - September 15, 2012
Lambar Labari: 2412071
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen msuulmi ta yi akkausar suka da yin Allawadai da fitar da fim dn batunci da Amurkawa suka yi da nufin wulakanta musulmi ta hanyar tozarta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen msuulmi ta yi akkausar suka da yin Allawadai da fitar da fim dn batunci da Amurkawa suka yi da nufin wulakanta musulmi ta hanyar tozarta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a cikin lokutan nan.

A wani labarin kuma Majalisar dokokin kasar Yemen ta bukaci sojojin Amurka su fice daga babban birnin kasar Sanaa.
Majalisar ta bukaci ficewar sojojin ne bayan sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayar da ke cewa ta aike da sojojinta zuwa birnin na Sanaa domin bayar da kariya ga ofishin jakadancinta a can, biyo bayan zanga zangar da mutanen birnin suka yi a harabar ofishin a jiya jumma’a. inda suke nuna fushinsu kan majigin nan na batunci ga manzon Allah.

Yansanda a kasar ta yemen dai sun kama mutane da dama sun tsare kan zanga zangar nuna fushin da suka yi kan batanci ga Musulunci.

Har’ila yau an gudanar da zanga zangar nuna fushi ga majigi mai batunci ga Musulunci a birnin Sudney na kasar Australia a gaban ofishin jakadancin kasar Amurca, Yan sandan gwamnatin Australia sun kama mutane da dama, wasu kuma sun samu raunuka a lokacin da yansanda suke kokarin tarwatsa su.

A nata bangaren majalisar dokokin kasar Afganistan ta yi Allah wadai da majigin wanda yake muzanta manzon Allah (s), kuma ta bukaci kasar Amurka ta haramta majaigin ta kuma gurfanar da wadanda suke da hannun wajen yin sa, kamar yadda majaliar ta bukaci da a janye dukaknin yarjeniyoyin tsaro da aka rattaba hannu kansu tsakanin Amurka da Afhanistan.

Tun bayan fitar da wannan fim na batunci ga manzon Allah da Amurkawa suka yi, al'ummomin musulmi na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a koina cikin fadin duniya, domin tabbatar wa Amurka cewa dukaknin jsulmi sun yi imanin cewa manzon Allah yana birbishinsu, kuma yin batunci a gare shi wuce dukkanin iyakoki ne a addinin muslunci.

1097919



















captcha