IQNA

Wajabcin Mayar da Martani Kan Fim Din Batunci Ga Manzon Allah

17:39 - September 18, 2012
Lambar Labari: 2414553
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin manyan malamin addinin musulunci a kasar Iraki ya y kakausar suka dangane da fitar da fim din batunci da aka yi ga manzon Allah tsiera da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka wanda hakan yake tabbatar da tsananin adawar da Amurkawa suke yi da addinin muslunci.


Kmafanindillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sautul Iraq cewa, Ayatollah Ozma Sayyid Kazim Hairi daya daga cikin manyan malamin addinin musulunci a kasar Iraki ya y kakausar suka dangane da fitar da fim din batunci da aka yi ga manzon Allah tsiera da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka wanda hakan yake tabbatar da tsananin adawar da Amurkawa suke yi da addinin muslunci da kuma musulmi.

Majalisar kasashen larabawan yankin tekun fasha ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allawadai da kai farmakin da ake yi kan ofisoshin jaadancin Amurka a kasashen musulmi, bayan fitar da fim batunci ga manzon Allah da Amurka suka yi.

Majalisar mai mambobi kasashe 6, wato Kuwait, Bahrain, Saudiyya, Qatar, Oman da kuma hadaddiyar daular larabawa, sun fiar da bayanin ne domin nuna rashin jin dadinsu dangane da martanin da musulmi suke mayarwa a cikin fushi kan Amurka ta hanyar kai farmaki kan ofisoshin jakadancinta da ke cikin kasashen musulmi.

Dukkanin kasashen 6, wato Kuwait, Bahrain Saudiyya, Qatar, Oman da kuma UAE sun haramta gudanar da irin wannan zanga-zanga ta nuna kyama ga gwamnatin Amurka a cikin kasashensu, tare da yin barazanar daukar matakai masu tsanani kan duk wanda ya nemi yin wani gangami kan abin da yake faruwa.

1099711


captcha