IQNA

Karfafa Ayyukan Soji Na Matukar uhimmancin Wajen Mayar Da Makircin Makiya

9:42 - September 19, 2012
Lambar Labari: 2414555
Bangaren siyasa, karfafa ayyukan soji na da matukar muhimamnci wajen mayar da makircin makiya a kowane lokaci domin ta hakan ne al'umma za ta iya tabbatar da abin da ta yi iamni das hi kuma take shirye ta bayar da rayuwarta a kansa bisa koyarwar addininta.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagoran juyin juya hali cewa, a safiyar yau ne Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kai ziyara jami'ar dakarun sojin ruwa na Imam Khumaini da ke garin Nushehr don halartar bikin yaye daliban jami'oin sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wannan bikin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da danyen aikin shirya fim din cin mutumcin Manzon Allah (s.a.w.a) da aka yi a Amurka inda ya ce: sakamakon masaniyar da al'umma suke da ita kan bakar siyasar ma'abota girman kai da yahudawan sahyoniya na adawa da Musulunci, don haka nan take su ka nuna yatsar zargi ga Amurka da wasu kasashen Turai. A saboda haka wajibi ne shugabannin wadannan kasashe su tabbatar (wa al'ummar musulmi) cewa ba su da hannu cikin wannan babban laifi ta hanyar hana faruwar irin wannan danyen aiki na hauka.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da gazawar da makiya Musulunci suka yi wajen fada da al'ummar Iran masu girma da kuma yunkurin farkawa ta Musulunci da ke faruwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: ‘Hakan shi ne dalilin da ya sanya makiya al'ummar musulmi aikata irin wadannan danyen aiki na hauka irin wannan lamari da ya faru na baya-bayan nan (wato shiryawa da kuma yada fim din cin mutumcin Ma'aiki).
Jagoran ya bayyana wannan lamari a matsayin daya daga cikin darussa na tarihi da za a iya dauka inda ya ce: Shugabannin gwamnatocin girman kai na duniya suna ikirarin cewa ba su da hannu cikin wannan danyen aikin, alhali kuwa sun ki su yi ko da Allah wadai ne da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Tabbas mu ba wai muna dagewa ne sai mun tabbatar da cewa suna da hannu cikin wannan danyen aikin ba, to amma irin halaye da dabi'un shugabannin Amurka da wasu na kasashen Turai su ne su ka sanya al'ummar musulmi suke ganin suna da hannu ciki. A saboda haka wajibi ne su tabbatar da cewa ba su da hannun ba wai kawai ta hanyar fadin hakan da fatar baki ba, face dai a aikace.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin kiyayyar Musulunci da ke tattare da cibiyoyin girman kan duniya, Jagoran ya bayyana cewar: Irin wannan kiyayyar ce take sanya ma'abota girman kai kin hana faruwar irin wannan danyen aikin kuma ba za su yi hakan ba.
Har ila yau kuma yayin da ya ke tabbatar da rashin gaskiyar abin da jami'an Amurka da na kasashen yammaci suke fadi na cewa ‘yancin hakkin fadin albarkacin baki ne ya ke hana su hana irin wannan cin mutumcin da ake yi wa Musulunci, Ayatullah Khamenei ya kafa hujja da wasu dalilai da suke tabbatar da karyarsu cikin wannan ikirari da suke yi yana mai cewa: "Daga cikin abubuwan da suke tabbatar da hakan shi ne jan layi da haramcin da kasashen yammaci suka sanya don hana duk wani abin da ke nuna adawa da tushen girman".
Daga nan Jagoran ya gabatar da wata tambaya ta cewa: Shin akwai wani da zai yarda da cewa a kasashen da ake amfani da dukkanin karfi da tursasawa wajen hana nuna adawa ga tushen girman kai, za su iya fadin cewa hana cin mutumcin ababe masu tsarki na Musulunci ya saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki?
Jagoran ya ci gaba da cewa: A da dama daga cikin kasashen yammaci, babu wani da zai iya yin jaruntakar sanya alamar tambaya kan hakikanin gaskiyar wannan lamari da ke cikin duhu na holocaust (kisan kiyashin da yahudawa suke da'awar an yi musu) ko kuma wani ya buga wani abin da zai nuna adawarsa da bakar siyasar ma'abota girman kai abar kyama irin su alaka ta luwadi da madigo. Ta ya ya za a iya cewa hakan ya wuce haddin ‘yancin fadin albarkacin baki, amma cin mutumcin Musulunci da ababe mai tsarki na Musulunci a matsayin ‘yancin fadin albarkacin baki?
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana Amurka a matsayin mai yada mulkin kama-karya a duniya sannan kuma yayin da ya ke ishara da irin goyon baya na shekaru aru-aru da Amurka ta ba wa tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Hosni Mubarak da Muhammad Ridha Pahlawi, tsohon sarkin kama karya na Iran da kuma sauran ‘yan mulkin kama karya na wannan yankin, cewa ya yi: "Tare da irin wannan bakin tarihi, ta ya ya za a yi Amurkawa su yi da'awar kokarin tabbatar da demokradiyya da goyon bayan ‘yanci (a duniya)?
Ayatullah Khamenei ya bayyana zanga-zangar da al'ummomi suka yi da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin siyasa da zamantakewa na Amurka a kasashe daban-daban a matsayin irin gagarumar kosawar da suka yi da bakar siyasar ma'abota girman kai da sahyoniyanci inda ya ce: Zukatan al'ummomi dai sun kosa da Amurka. A saboda haka ne daga lokacin da aka samu faruwar wani abu irin abin da ya faru na baya-bayan nan (na shirya wannan fim na cin mutumcin Ma'aiki), nan take irin wannan kiyayya da kyama take fitowa fili.
A karshen wannan bangare na jawabin nasa, Jagoran ya jaddada cewar: Ko shakka babu hasken Musulunci a gaban fadar da ma'abota girman kai suke yi da wannan addini na Ubangiji zai ci gaba da bayyana ne sama da na shekarun baya, sannan kuma nasara tana tare da wannan al'umma ta Musulunci ne.
Har ila yau kuma a wani bangare na jawabin nasa a wajen wannan biki na yaye daliban jami'oin sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ba su lambar girma, Jagoran juyin juya halin Musuluncin kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran ya bayyana kasantuwa cikin dakarun kasar Iran ciki kuwa har da sojoji a matsayin wani lamari abin alfahari, daga nan sai ya ce: matasa masu girma da suka shigo wannan fagen cikin so da kauna da kuma basira, ko shakka babu za su sami jinjinawa na al'umma, daukaka ta duniya da kuma lada ta Ubangiji.
Jagoran ya bayyana Iran a matsayin wani kogi na kaunar ci gaba da kuma yunkuri na samar da sabbin abubuwa kuma masu amfani inda ya ce: Gwargwadon yadda shekaru suka gushe, gwargwadon yadda muhimmanci da kimar da ke cikin kokari wajen Jamhuriyar Musulunci da kuma karfafa wannan gagarumin gini zai dada fitowa fili, wanda a wannan fagen kuwa dakarun soji suna da wani gagarumin nauyi a wuyansu.
An fara gudanar da wannan bikin ne bayan isowar Jagoran da rera taken Jamhuriyar Musulunci ta Iran sannan kuma kai ziyarar makabartar shahidai don jinjinawa da kuma girmama shahidan Musulunci da juyin juya halin Musulunci da kuma kasar Iran, sannan kuma ya wuce ta gaban jerin sojojin da suka taru a wajen bikin. Har ila yau kuma Jagoran ya ba wa wasu daga cikin iyalan shahidai lambobin girma.
1101531





















captcha