Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, malaman addinin muslunci a kasar Mauritania sun bukaci da haramta fim din nan da aka fitar na cin zarafin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka domin ta hakan ne za a tabbatar da cewa an kare mutunci da martabar addinin muslunci.
Sojojin Siriya suna ci gaba da tsarkake yankunan kasar daga 'yan ta'adda tare da halaka da dama daga cikin 'yan ta'addan a yau litinin, kafar watsa labaran gwamnatin Siriya "Sana" ta bayyana cewar a yau litinin sojojin kasar sun kai farmaki kan yankin Saifud Daula da ke garin Halab da yankin da ke kusa da kan iyaka da kasar Turkiyya, inda suka yi nasarar halaka 'yan ta'adda da dama, tare da kwasan ganimar makamai manya da kanana da aka shigo da su cikin kasar daga kasashen ketare domin karfafa ayyukan ta'addanci a kasar.
Har ila yau sojojin kasar ta Siriya sun kaddamar da hare hare kan tawagar 'yan ta'adda a yankin Babul da ke garin Halab inda suka kashe 'yan ta'adda 34. Haka nan sojojin gwamnatin Siriya sun tarwatsa wata wasu motoci da suke dauke da 'yan ta'addan a yankin Kufru Humur.
Kamar yadda sojojin suka kai farmaki wata maboyar 'yan ta'addan a yankin Al-Fara'yah da ke garin Hama, inda suka halaka 'yan ta'adda akalla 8 tare da jikkata wasu da dama, kuma wasu daga cikin 'yan ta'addan sun mika kansu ga sojojin.
1100038