Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa fitowar da dukaknin musulmi suka yia dukaknin kasashen duniya domin nuna rashin amincewarsu da abin da ya faru an cin zarafin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi hakn ya tabbatar da gagrumin ci gaban da musulmi suka samu wajen kara fahimta da yin riko da addininsu sakamakon hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar wajibi ne Amurka da wasu kasashen yammaci su tabbatar wa al’ummar musulmi cewa ba su da hannu cikin fim din cin mutumcin Musulunci da aka shirya a Amurka a aikace ba wai kawai ta hanyar magana ta fatar baki ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin yaye daliban jami’oin soji na Iran a yau din nan inda ya ce shugabannin gwamnatocin girman kai na duniya suna ikirarin cewa ba su da hannu cikin wannan danyen aikin, alhali kuwa sun yi su yi allah wadai da shi da kuma daukan matakan da suka dace wajen hana faruwarsa.
Ayatullah Khamenei ya ce wannan cin mutumcin da aka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo ne sakamakon gazawar da suka yi wajen fada irin karbuwar da Musulunci yake samu da kuma farkawar da al’umma suke yi yana mai cewa karya ce ‘yan siyasar Amurka suke yi na cewa ‘yancin hakkin fadin albarkacin baki ne ya hana su daukan mataki kan wannan cin mutumci da aka yi wa Musulunci alhali kuwa suna amfani da karfi da tursasawa wajen hana duk wani nuna adawa da siyasar girman kan duniya da kuma hatta sanya alamar tambaya kan lamarin ikirarin kisan kiyashin da aka yi wa yahudawa.
Haka nan kuma yayin da ya ke magana kan hare-haren da aka kai wa ofisoshin jakadancin Amurka da wasu cibiyoyinsu a kasashe daban-daban na duniya, Jagoran cewa ya yi hakan ya biyo bayan bakar siyasar Amurkan ne da kuma yadda al’ummomin suka kosa da irin wannan bakar siyasa ta Amurkan.
1100966