Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na onislam, cewa an soke wata dokar hana saka hijibi a wata makarantar a kasar philipines sakamakon kin amincewa da hakan da wata kotu a kasar ta nuna da kuma yadda wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama suka mike tsaye domin kare hakkonin musulmi na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Jamus na da musulmi da yawansu ya haura miliyan hudu a fadin kasar, saboda haka wannan jami’a ta dauki nauyin bayar da karatu kan muhimman abubuwan da ya kamata masu jagorancin masallatai su koya kafin fara limanci, wanda kuma malaman addinin muslunci ne za su koyar da su a jami’a bisa tsari na karatun digiri.
Gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci, hakan na da matukar alfanu ga musulmi.
A halin yanzu akwai limaman masallatai sama da dubu takwas a fadin kasar Jmaus, kuma akasarinsu mutanen kasar Turkiya dasuke je kasar daga bangaren gwamnatin Turkiya, wadanda ba su da cikakkiyar masaniya kan harshen jamusanci da ake magana da shi a kasar. 1102266