Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin muhimman ayyukan kafofin yada labarai na kasashen musulmi shi ne yada tunani jihadi da kuma gwagwarmaya domin tabbatar da adalci a bayan kasa da kuma nuna kiyayya da duk wani nauin zalunci da danniya da ake yiwa al’ummomin duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa na cikin gida cewa, shugaban majalisar shawarar muslunci Ali Larijani ya bayyana cewa, daya daga cikin muhimman ayyukan kafofin yada labarai na kasashen musulmi shi ne yada tunani jihadi da kuma gwagwarmaya domin tabbatar da adalci a bayan kasa da kuma nuna kiyayya da duk wani nauin zalunci da danniya da ake yiwa al’ummomin duniya baki daya.
Wanda ya jagoranci sallar juma’ar birnin Tehran a yau din nan ya bayyana cewar sadaukarwa da sanin ya kamatan al’ummar Iran a lokacin kallafaffen yaki na shekaru 8 da gwamnatin Saddam ta kallafa musu ya bude wani sabon shafi cikin tarihin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke cike da ababen alfahari. Hujjatul Islam wal muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da hudubar sallar juma’a a masallacin juma’ar Tehran inda yace a lokacin kallafaffen yaki da dama daga cikin kasashen duniya sun taimaka wa Saddam Husain da makamai da kuma daukan matsayar cutar da Iran, to amma sakamakon imani da Allah da kuma jagoranci na marigayi Imam Khumaini (r.a) dakarun kasar Iran sun tilasta wa makiya ja da baya sannan kuma suka sami nasara a kansu. Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan cin mutumcin da aka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a) a Amurka da kasar Faransa, Shehin malamin ya bayyana bakin cikin da ma’abota girman kai da yahudawan sahyoniya suke ciki sakamakon yadda duniya take komawa ga Musulunci, irin yadda al’ummomin yankin nan suke daukan juyin juya halin Musulunci na kasar Iran a matsayin abin koyi da kubucewar mulki daga hannun ‘yan amshin shatansu a yankin nan sakamakon yunkuri da farkawa ta Musulunci da ke kadawa a matsayin abubuwan da suka sanya su cin mutumcin Ma’aiki din. Har ila yau kuma yayin da ya koma kan matsin lambar da kasashen yammaci suke wa Iran musamman kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, Hujjatul Islam Siddiqi ya ce ko da wasa wadannan matsin lambar ba za su sanya Iran ja da baya daga tafarkin da ta rika ba.
1105064