Bangaren kasa da kasa, ya rataya kan kafofin yada labarai na kasashen musulmi su samar da wasu hanyoyi na fitar da fina-finai da shirin da zai kara fito da hakikanin sirar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka domin kalubalantar wadanda suke cin zarafin addinin muslunci.
Kamfanin diallancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam, cewa da dama daga cikin masana suna ganin cewa ya rataya kan kafofin yada labarai na kasashen musulmi su samar da wasu hanyoyi na fitar da fina-finai da shirin da zai kara fito da hakikanin sirar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka domin kalubalantar wadanda suke cin zarafin addinin muslunci ta hanyar cin zarafin wannan manzo mai tsarki.
A yau yahudawan sahyuniya sun rufe kofar shiga masallacin Qods domin hana palastinawa yin sallah a cikinsa hakan ya zo ne a wani mataki da mambobin jamiyar likud ta masu tsatsauran ra’ayi daga cikinsu ta dauka domin tsokanar musulmi mazaunan birnin, da sauran musulmi masu sauran lamiri a cikin kasashen musulmi da na larabawa.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya. 1105025